TARIHIN BITCOIN PIZZA DAY
Bitcoin pizza dayπ
TARIHIN BITCOIN #PIZZA_DAY.
May 22nd Shekara sha biyu kenan da fara cinikayya da #Bitcoin ta zahiri, wanda akayi ranar laqabi #Bitcoin_pizza_day.
Shekara 12 kenan floridan programmer LANSZLO HANYECZ wanda ya fara cinikayya ta zahiri da #bitcoin inda ya siya pizza guda biyu.
Hanyecz ya sanar a cikin platform na Bitcointalk.org a ranar 18-may-2010 cewar yanaso ya siya pizza da kudin bitcoin inda ya bayyana cewar guda biyu yake buqata , inda ya bayyana cewar a shirye yke ya biya bitcoin guda dubu goma 10,000 π (kaji rashin sani) ga duk wanda zaiyi masa placing order na pizza guda biyu yazo ya amshi bitcoin guda 10,000 π€£.
Wannan rana ta 18 ga watan mayu 2010 haka ta wuce ba wanda y a saurareshi akan kudurin nasa na siyan pizza da bitcoin, a haka dae harya fara yanke qauna akan qudurin nasa.
Sae ranar 22 ga watan mayu 2022, ne aka samu wani matashi suna JEREMY STURDIVANT mai shekara 19 a wancan lokacin ya yarda zai kawo masa pizza akan bitcoin dubu goma wanda a wancan lokacin darajarsa batafi $41 ba.
Aikuwa matashin nan ya cika alkawarinsa yayi placing order ta kawo wa Hanyecz pizza dinsa guda biyu har wajensa.
A wannan lokacine Hanyecz ya dauki hoton nan dake kasa ya rubuta cewar " Inaso in sanar daku cewar nayi nasarar siyan pizza da bitcoin 10,000". (Muna tayaka jimamiπ)
Bayan shekaru kadan Hanyecz yayi nadamar abunda ya aikata na siyan pizza da $btc 10,000.
Da ace ya rikesu harzuwa yau da darajarsu takai $293,800,000 π±π±π± idan kuma akai la'akari da mafi kololuwar farashin da ya ta6a xuwa (ATH) darajar zatakai kimanin $692,000,000 π
#cryptocurrency #crypto #bitcoinpizzaday #nft #metaverse #CRYPTOFXMINDSET

Comments
Post a Comment